Tawagar MDD dake kasar Libya a ranar Lahadin nan ta mika tayi ga kungiyoyin dake gaba da juna a kasar da su zauna a tattauna a ranar Litinin mai zuwa 29 ga wata domin kawo karshen tashin hankalin da kasar ke fuskanta.
Tawagar MDD dai ta mika wannan tayi ne da nufin dukkan wakilan kungiyoyi daban daban na kasar za su zauna a teburin shawarwari a wannan rana ta 29 ga wata domin samar da maslaha. A lokacin tattaunawar, ana sa ran tabo batun yarjejeniya a kan rana da kuma wurin da ya kamata a yi bikin mika ragamar shugabanci daga tsohuwar majalissar babban taro ta kasar zuwa sabuwa majalissar dokokin kasar.
Libya dai tana ta fuskantar tashin hankalin siyasa, sannan yanzu tana tsaka mai wuya tsakanin majalissar dokoki guda biyu dake hamayya da junan su, da ma gwamnatin gaba daya.
A yadda shirin mika mulkin na kasar Libyan ya nuna, sabuwar majalissar dokoki da aka zaba, da majalissar wakilai sun riga sun maye gurbin tsohuwar majalissar babban taron kasar. Sai dai kungiyar masu kaifin kishin addini dake dauke da makamai Libyan Dawn, wadda a 'dan cin lokacin ta cimma harin soji da dama a birnin Tripoli, tana goyon bayan tsohuwar majalissar dokokin, ta kuma kafa sabuwar gwamnati maimakon sabuwar da aka zaba. (Fatimah)




