in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Xinjiang ta yanke wa mutanen dake da hannu a kisan wani limami hukunci
2014-09-29 09:44:23 cri

A ranar Lahadi ne wata kotu a Xinjiang da ke nan kasar Sin ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa yayin da mutum daya kuma aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai, sakamakon zargin da ake musu na laifin kashe wani fitattacen limami a watan Yuli.

Matsakaiciyar kotun al'umma da ke Kashgar a yankin na Xinjiang da ke nan kasar Sin, ta yanke wa Gheni Hasan da Nurmemet Abidilimit hukuncin kisa ne bisa laifin kafa kungiyoyin ta'addanci da jagoranta da kuma aikata kisan kai, yayin da shi kuma Atawulla Tursun aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai bisa zargin shiga kungiyoyin ta'addanci da aikata kisan kai.

Kotun ta ce, a ranar 30 ga watan Yuli ne Nurmemet Abidilimit da wasu mutane biyu, suka halaka Jume Tahir a wajen masallacin Id Kah dake Kashgar, kana 'yan sanda suka harbe mambobin kungiyar guda biyu har lahari yayin da suke farautar 'yayan kungiyar.

Jama'a da dama ne suka halarci zaman kotun. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China