in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Xinjiang sun yi Allah wadai da kisan babban limami da masu kaifin ra'ayin addini suka yi
2014-08-01 10:06:28 cri

Kabilu daga sassa daban daban sun yi Allah wadai da kisan Jume Tahir, babban limamin masallaci mafi girma a kasar Sin dake jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta da masu kaifin ra'ayin addini suka aikata a ranar Laraba.

Shugaban kungiyar lauyoyi na jihar Xinjiang Sang Yun ya ce, masu kaifin addinin sun kashe wannan dattijo mai kula da addinin, daukacin lauyoyin wannan yankin suna nuna matukar bakin cikinsu da takaici, a cewarsa, wannan halayya na 'yan ta'adda ya nuna a fili mugun yanayin ayyukan ta'addanci da ake aikatawa a cikin al'umma.

Shi ma Su Ning, mataimakin shehun malami a jami'ar kudi da tattalin arziki dake Xinjiang, ya ce, kisan wannan babban malami mai imani ya sake nuna mugun yanayin ta'addanci na yaki da cin zarafin bil adama.

A nashi tsokacin, Wang Yunhui, wani ma'aikacin gwamnati a birnin Urumqi ya ce, masu kisan kai sun sake aikata wani babban laifi a cikin musulunci, wanda addini ne na zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa daga kungiyar addinin musulunci ta wannan yankin, ta bayyana cewa, dukkan musulmai ya kamata su fahimci illar dake cikin ayyukan ta'addanci, da kuma mummunan halin da masu kaifin addini suke kawo wa zamantakewar jama'a. Sanarwa ta ce, kisan da aka yi wa malam Jume Tahir, babban laifi ne wanda ko kadan addinin musulunci ba ta yarda da shi ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China