Wasu kotuna 3 sun zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 13, a lardin Xinjinag mai cin gashin kansa dake arewa maso yammacin kasar Sin, bayan da aka tabbatar da zargin da aka yiwa mutanen na shiryawa, da kuma aiwatar da ayyukan ta'addanci.
Kotunan na Aksu, da Turpan da Hotan sun yankewa mutane hukuncin ne a jiya Litinin, bayan samun cikakkun shaidu dake tabbatar da wadanda ake zargin sun aikata laifuka 7, da suka hada da kera ababen fashewa, da sufurin su, tare da amfani da su wajen hallaka mutane da barnata dukiyoyi. Tuni dai babbar kotun kolin kasar Sin ta amince da wannan hukunci kamar yadda dokar kasar ta tanada.
A wani labarin mai alaka da wannan, wata kotu dake zaman ta a Urumqi ta yankewa wadanda ake zargi da kai harin Tian'anmen dake nan birnin Beijing hukuncin kisa. Kotun ta yankewa mutanen su 3 hukuncin ne, bayan da ta tabbatar da zargin da ake musu, na kai hari a filin na Tian'anmen cikin watan Oktobar bara.
Hakan dai na zuwa ne bayan da mahukuntan kasar ta Sin suka daura yaki da ayyukan ta'addanci, karkashin wani shiri na shekara guda, biyowa bayan harin ranar 22 ga watan Mayun, da wasu masu tada kayar baya suka kai wata kasuwa dake birnin Urumqi, wanda ya sabbaba rasuwar mutane 39, tare da jikkata mutane 94. (Saminu)