in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za'a lamuncin kisan babban limamin Xinjiang da aka yi ba
2014-08-01 10:17:42 cri

Kisan da aka yi wa Jume Tahir, sanannen malamin addinin musulunci a jihar Xinjiang ta kasar Sin, wani kalubale ne da 'yan ta'adda suka kawo wa ka'idojin zaman al'umma cikin lumana wanda kuma ba za'a lamunta ba.

Yan Sanda sun harbe mutane biyu, suka kuma kame mutum guda a kokarin da suke yi na binciken wannan danyen aiki na kisan limamin babban masallaci na kasar Sin baki daya wato masallacin Id Kah a birnin Kashgar dake jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta.

Malam Jume Tahir, mai shekaru 74 da haihuwa, an kashe shi ne a ranar Laraba bayan ya kammala jagorancin sallar asuba. Binciken 'yan sanda ya nuna cewa, wadanda ake zargin suna da kaifin addinin, don haka kisan gilla da 'yan ta'addan da masu kaifin addini sun aikata, wani laifin ne da ya take hakkin bil adama da ya wuce tunanin kowa. Ba za'a amince da shi ba a kowace kasa, ko al'umma a duk fadin duniya.

Haka kuma ya zama wani abin tunatarwa na cewa, dole ne a dauki kwararrun matakai na shawo kan wannan ta'addanci wanda ba za'a yi sanyin jiki ba a ciki.

Ta'addanci ya yi matukar keta dokokin kasar Sin, don haka dole ne masu aikata shi su fuskanci hukunci. Wannan kisan gilla na baya bayan nan ya kara nuna mummunan yanayin ta'addanci, wariya da kaifin kishin addini. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China