Shugabannin kasashen Afrika shida ne za su halarci wani zaman taro na kwamitin zaman lafiya da tsaro (CPS) na kungiyar tarayyar Afrika (AU) da zai gudana a birnin Nairobi na kasar Kenya domin tattauna kan barazanar tsaro a nahiyar, in ji ministan harkokin wajen kasar Kenya a ranar Litinin.
Ministan ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shugabannin Chadi, Nijar, Najeriya, Somaliya, Tanzaniya da Uganda sun tabbatar da zuwan nasu a wannan babban dandali na yini guda da za'a fara a ranar Talata a Nairobi.
Makasudin wannan taro shi ne kaddamar da wani cikakken nazari kan wannan matsala da kokarin da kungiyar AU take yi a halin yanzu domin yaki da ta'addanci a nahiyar Afrika bisa tsarin dokoki da matakan aikin da suka dace na kungiyar tarayyar Afrika AU, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)