Rundunar tsaron sojoji ta tarayyar Nijeriya na ci gaba da daukar matakai na yaki da yayan kungiyar Boko Haram, masu tada kayar baya. Wata sanarwa daga hedkwatar ma'aikatar tsaro ta Nigeria ta ce, dakarun Nijeriyar sun murkushe wani shirin ramuwar gayya, wanda 'yan kungiyar ta Boko Haram ke shirin aiwatarwa a garin Konduga, mai nisan kilomita 50 daga Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno, garin na Konduga a makon da ya wuce ya kasance cikin tashin hankali bayan da aka yi wani kazamin artabu na awowi 12, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar masu tada kayar baya fiye da dari daya.
A kuma lokacin gumuzun na makon da ya wuce ne rundunar sojin Nijeriyar ta kame wadansu motoci kirar Hilux, da kuma motar sulke da makamai da albarusai. (Suwaiba)