in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya ba da ahuwa ga fursunoni 1104
2014-07-30 14:23:49 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi wa wasu fursunoni kimanin 1104 ahuwa da ake tsare da su a cikin gidajen yarin kasar, in ji wani babban jami'in gwamnatin kasar.

Wata sanarwa da mataimakin ministan cikin gida, James Agalga ya sanya wa hannu, ta nuna cewa, shugaban kasa ya ba da ahuwa bisa aya mai lamba 72 ta kundin tsarin mulkin kasar Ghana, yayin bikin tunawa da cikon shekaru 54 da kasancewar kasar ta Ghana.

Bisa wannan ahuwa, fursunoni 21 da aka yanke wa hukuncin kisa da aka tsare da su fiye a kalla shekaru goma, an sassauta hukuncinsu zuwa zaman yari.

Haka ayar kundin tsarin mulki ta nuna cewa, shugaban kasa na daukar matakin bisa tuntubar kwamitin dattawa dake hurumin ba da ahuwa ga duk wani mutum da ake yanke wa hukunci bisa sharuden doka.

A cewar sanarwa, kwamitin ma'aikatan gidajen yarin kasar Ghana ne ya gabatar da shawarwari ga shugaba Mahama da wannan ahuwa ta dukkan fadin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China