A kalla mutane 115 ne aka tabbatar da mutuwarsu lokacin da wani gini ya rushe a jihar Ikko dake tarayyar Nigeriya, kamar yadda wani jami'in kasar Afrika ta Kudu ta sanar a ranar Litinin din nan.
Jeff Radebe, minista a fadar shugaban kasar ya ce, daga cikin mutanen, 84 'yan kasar Afrika ta Kudu ne.
Shi dai wannan gini na wata mujami'a ya rushe ne a ranar 12 ga wannan watan da muke ciki lokacin da ya cika da mabiya masu ibada. (Fatimah)