in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Afirka ta Kudu 67 ne suka rasu sakamakon faduwar gini a Legas
2014-09-17 10:36:48 cri

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya bayyana jimami game da rasuwar 'yan kasarsa 67, sakamakon faduwar ginin nan mallakar majami'ar Synagogue dake jihar Legas a tarayyar Najeriya.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta jajantawa iyalan mamatan, da ma daukacin 'yan kasar bisa rasuwar wadannan mutane. Sanarwar ta kuma nuna alhini game da karin wasu 'yan kasar da suka ji raunuka yayin rubzawar ginin a ranar Juma'ar da ta gabata.

Shugaba Zuma ya ce, ya kadu matuka da samun wannan labari, musamman duba da cewa wannan ne karon farko a tsahon lokaci, da 'yan kasar da dama suka rasu a ketare sakamakon wani hadari.

Ya ce, gwamnatinsa na shirin baiwa iyalan wadanda hadarin ya ritsa da su damar zuwa jihar ta Legas domin tantance 'yan uwansu. Baya ga tallafi da ya ce gwamnatin ta sa za ta ba su gwargwadon hali.

A daya hannun kuma, a madadin al'ummar Afirka ta Kudu, shugaba Zuma ya mika sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Najeriya, da ma na sauran kasashe da suka rasa mutanensu sakamakon rushewar ginin.

Amma hukumar NEMA mai ba da agajin gaggawa a Najeriya dai ta ce, ya zuwa ranar Talata, mutane 57 ne ta hakikance sun mutu sakamakon aukuwar wannan hadari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China