in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda faduwar gini a jihar Legas ya hallaka ya karu zuwa 80
2014-09-18 10:01:31 cri

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta tarayyar Najeriya Ibrahim Farinloye, ya ce, ya zuwa ranar Laraba 18 ga wata, adadin wadanda faduwar ginin nan na jihar Legas ya hallaka ya kai mutane 80.

Farinloye ya kara da cewa, baya ga wadanda aka hakikance da rasuwarsu, akwai kuma wasu 131 da jami'an hukumar suka tseratar. Ko da yake bai fayyace kasashen mutanen da wannan gini ya fadawa ba.

Tun dai a ranar Talatar da ta gabata, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya gabatar da sakon ta'aziyyar al'ummar kasarsa su 67, wadanda a cewarsa suna cikin wadanda hadarin faduwar ginin na jihar Legas ya ritsa da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China