Bayan gyara kan hasashen da aka yi cikin rahoton farko, wanda binciken bankin duniya ya gudanar, an gano cewa a shekara ta 2011 an samu karuwa ta kishi 5.9 cikin 100.
A yanzu dai bunkasar tattalin arzikin kasar a shekara ta 2012 zai kasance kasa da kishi 7.2 cikin 100, sai dai kuma zai kai sama da 5.7 cikin 100 kamar yadda gwamnatin kasar Botswana ta yi nata hasashe a karshen shekara ta 2010. A yanzu dai ana jiran sakamako ya fito a watan Maris daga ma'aikatar kididdiga da lisafi ta kasar Botswana, na dukkan alkalumman binciken da aka gudanar kan abun da kasar ke samu ta fannin tattalin arziki na shekara ta 2011.
Bincike na karshe da ya gudana, an yi shi a kan dukan wani cikas da a kan iya samu a game da bunkasar tattalin arziki, da kuma gano ko zai iya kawo rashin nasara ga lamuran gwamnatin kasar Botswana, ko kuma kawo tsaiko ga bunkasar tattalin arzikin kasar a shekara ta 2012.
Rahoton bankin duniya da take yi duk shekaru biyu ya nuna cewa, babban kalubale ga kasar Botswana a game da bunkasar tattalin arzikinta a wannan shekara ta 2012, zai kasance ya zo ta fannin raguwar kudin shiga daga bangeren kayayyakin da ake amfani da su wajen sarrafa abubuwa. (Abdou Halilou)