in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda suka rasu sakamakon faduwar gini a Legas ya karu zuwa 49
2014-09-16 09:36:32 cri

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa a Tarayyar Najeriya Ibrahim Farinloye, ya ce, adadin mutanen da aka tabbatar sun rasu sakamakon faduwar ginin nan na jihar Legas ya karu zuwa 49.

Farinloye ya kuma ce, an samu damar ceton mutanen 130 daga baraguzan ginin mallakar majami'ar Synagogue dake unguwar Ikotun a wajen birnin Ikko.

Tuni dai babban limamin cocin Pastor Temitope Joshua, ya alakanta faduwar ginin a ranar Juma'ar da ta gabata da wani jirgi mai saukar ungulu, wanda ya yi zargin ya kewaya ginin sau da dama kafin faduwarsa.

Pastor Joshua wanda ya nuna wa manema labaru wani faifan bidiyo na tsahon mintuna 3, ya nace cewa, wancan jirgi ne ya haddasa rubzawar ginin mai hawa 6.

Yayin da jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ke ci gaba da aikin ceto, rahotanni na cewa, mai yiwuwa ne akwai karin mutane dake binne karkashin ginin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China