Majalissar dokokin kasar Libya dake da helkwata a Tobruk, ta ce, ta sauke babban gwamnan bankin kasar Saddiq al-Kabir daga mukakinsa, a wani mataki na abin da ta kira gudanar da sauye-sauye a fannin hada-hadar kudi.
Wata sanarwa da majalissar ta fitar, ta rawaito mai magana da yawunta Faraj Abo Hashem na cewa, za a kuma binciki korarren gwamnan bankin game da yadda ya gudanar da ayyukansa a baya.
Hashem ya kara da cewa, wakilan majalissar 94 cikin 102 ne suka halarci zaman da ya tabbatar da daukar wannan mataki. Ko da yake a hannu guda wasu na kallon hakan a matsayin wata kullalliya, a kokarin da sabuwar majalissar ke yi na samawa kai kudaden shiga, ba tare da bi ta karkashin tsohuwar majalissar dokokin kasar ba.
To sai dai fa a daya bangare Al-Kabir, wanda aka zarga da tallafawa tsohuwar majalissar kasar ya ce, ba zai sauka daga mukamin nasa ba.
Kasar Libya dai na shan fama da matsalolin siyasa tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011 da ta gabata, inda a yanzu haka take da majalissun dokoki da gwamnatoci biyu masu adawa da juna. (Saminu)




