Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yi allahwadai da tagwayen hare-haren bam din da aka kai a garin Kaduna wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 70, tare da da jikkata mutane da dama.
A cikin wata sanarwa da shugaban ya bayar, ya yi allahwadai da hare-haren da ake ganin an kai su ne da nufin halaka tsohon shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari, da kuma fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Dahiru Bauchi.
Shugaba Jonathan ya umarci 'yan sanda da hukumomin tsaro, da su dauki dukkan matakan da suka wajaba don zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki don ganin sun fuskanci hukunci.
Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram da ke hankoron kafa shari'ar musulunci a kasar da ke yammacin Afirka. (Ibrahim)