Gwamnatin Afrika ta Kudu na mai da martani kan damuwarta dake da nasaba da sabbin dokokin da suka shafi takardun Visa, da aka yi ta nuna suka kansu sosai domin suna janyo matsala a fannin yawon bude ido, in ji ministan yawon bude idon kasar, Derek Honekom a ranar Alhamis.
Bayan wata tattaunawa tare da ministan cikin gidan kasar Afrika ta Kudu, Malusi Gigaba, an yi wasu gyare-gyare ga sabbin matakan domin rage kaifin illar wadannan matakai ga yawon bude ido, in ji mista Honekom a yayin taron dandalin tattalin arzikin yawon bude ido a nahiyar Afrika dake gudana a birnin Cap. (Maman Ada)