Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar hadin kan Afirka ta AU uwar gida Nkosazana Dlamini Zuma, ta bayyana matukar damuwa game da juyin mulkin da sojoji suka gudanar a Lesotho, lamarin da ya janyo tabarbewar yanayin siyasa a kasar.
Zuma wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta kuma bayyana bukatar da ake da ita ga daukacin bangarorin kasar masu adawa da juna, da su mai da hankali ga warware banbance-banbancen dake tsakanin su karkashin tanajin kundin mulkin kasar.
Kaza lika Zuma ta jaddada rashin amincewar AU da dukkanin wani mataki dake da nasaba da hambarar da gwamnatin kasar ta Lethoso ta haramtacciyar hanya, tana mai cewa, kungiyar ba za ta lamunci duk wani shiri na kwatar mulki da karfin tuwo ba.
A daya hannun, shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta AU ta godewa kungiyar bunkasa kasashen kudancin Afirka, bisa kokarinta na shawo kan matsalolin da kasar ta Lesotho ke fuskanta, tare da kokarin dawo da doka da oda a kasar. (Saminu)