in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na neman 'yan sanda 20 da suka bace
2014-09-10 09:50:04 cri

A kalla 'yan sanda 20 aka rasa duriyarsu tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta kai wani hari kan ayarin 'yan sanda na sintiri (PMF) a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, in ji safeto janar 'yan sandan Najeriya, Suleiman Abba a ranar Talata, a yayin wata hira da manema labaru, bayan ganarwarsa da mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo a Abuja, babban birnin Najeriya.

Cikin jami'an 'yan sandan 35 dake makarantar horar da 'yan sanda da aka rasa duriyarsu, kila wasu sun koma makaranta, ko sun koma gidajensu.

Makarantar horar da 'yan sanda masu sintiri dake Gwoza, ta fuskanci wani harin 'yan ta'adda da ake zaton 'yan Boko Haram ne a ranakun 7 da 20 ga watan Agusta.

Ana kyautata zaton wasu 'yan sanda za su iyar tserewa daga makarantarsu, dalilin tsoron kadda maharan su sace su, a cewar wasu masu fashin baki. Haka kuma fiye da mata 'yan makaranta 200 na garin Chibok, aka rasa labarinsu tun bayan da mambobin Boko Haram suka kai wani hari a inda 'yan matan suke kwana a cikin watan Afrilu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China