Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana a ranar Talata, da shirin gina wata masana'antar hada motoci, bisa jarin da ya cimma Rands miliyan 600, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 57, aikin da kamfanonin kasar Sin suka dauki nauyin zuba kudinsa, ya kasance wani babban misalin dake bayyana kyakkyawar dangantakar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu.
Wannan masana'anta za ta kawo babban taimako ga cimma manyan maradun cikin gida na cigaban tattalin arziki, da na jama'ar kasar, in ji mista Zuma a cikin wata sanarwa.
Masana'antar dake yankin unguwar kamfanoni na Coega (ZDI) dake Port Elizabeth a gabashin gundumar Cap, ta samu jarin hadin gwiwa na kamfanin kera motoci na kasar Sin wato China's First Automabile Works (FAW) Group Corporation, da kuma asusun cigaban Sin da Afrika. A halin yanzu masana'antar za ta rika hada motoci dubu biyar a ko wace shekara.
Zuba jarin kamfanin FAW na da babban muhimmanci ga makomar tattalin arzikin kasar, musammun ma ga shiyyar Baie Nelson Mandela da yankin Eastern Cape ta fuskar samun jarin waje kai tsaye, wanda shi kuma zai samar da guraben ayyuka yi cikin dogon lokaci, samun horo da cigaban kwarewa, in ji mista Zuma. (Maman Ada)