Dubban fararen hula ne suka kaura daga gidajensu bayan 'yan sa'o'i na gumurzu tsakanin jami'an tsaron Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram a wani garin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya.
A ranar Litinin, sojojin Najeriya sun murkushe wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a kokarin kwace garin Bama mai yawan jama'a, dake da tazarar kilomita 78 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Majiyoyi dake wannan yanki sun rawaito cewa, fiye da mazauna wurin dubu uku ne suka gudu daga gidajensu, sannan suka samu mafaka a wasu yankunan dake makwabtaka da su.
Wani ofisa ya shaidawa Xinhua cewa, maharan sun isa Bama cikin motoci, kana suka kai hari a wani wurin ajiyar makaman soja. Wannan lamarin ya tilastawa hukumomin soja yin amfani da jirgin yaki kan wadannan wurare.
An kashe mayakan Boko Haram da dama, haka mun rasa sojoji a ranar Litinin, in ji wata majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.
Hedkwatar tsaron Najeriya dake Abuja, ta tabbatar da wannan gumurzu na Bama, amma kuma ta ce, har yanzu ba ta da tabbatanci kan yawan mutanen da suka mutu, ko suka ji rauni. (Maman Ada)