in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeria sun yi musayar wuta da mayakan Boko Haram a Borno
2014-09-02 10:58:05 cri

Rahotanni sun nuna cewar, an ji karar harbe-harben bindiga mai tsanani daga wuraren da ake bata kashi a jihar Borno, tsakanin rundunar sojojin Nigeria da kuma wasu da ake zaton 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Wani mazaunin Goneri Ibrahim Mohammed dake cikin Bama, wanda shi ne gari na 2 mafi gima a jihar Borno, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewar, ana ci gaba da jin karar manyan bindigogi a sakamakon arangamar da ake yi tsakanin dakarun gwamnatin Nigeria da na 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Ibrahim Mohammed, wanda shugaban kungiyar sa kai ta matasan Goneri ya ce, tun farko sojojin Nigeria sun kawo dauki nan take a yayin da mazauna garin suka tuntube su suna neman a kawo masu taimako ta wayar tarho, a sakamakon harin na Boko Haram, kuma kamar yadda ya ce, akwai yiwuwar jama'a da dama sun jikkata a sakamakon arangamar.

Ya ce, matasan Goneri da ke da nisan kilomita 80 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun hada karfi da sojojin gwamnatin kasar domin samun nasarar murkushe hare-haren kungiyar Boko Haram. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China