Majiyoyin tsaro da kuma ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa, tagwayen hare-haren bam din da aka kai a garin Kaduna da ke arewacin kasar, sun halaka sama da mutane 70. Ko da yake kwamishinan 'yan sandan jihar Shehu Umar ya ce, bisa alkaluman da suka samu, mutane 39 ne suka mutu.
Kwamishinan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kama wani mutum da ya yi shigar mata a wurin da lamarin ya faru. A cewarsa, bam na farko da ya fashe ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25, yayin da na biyun ya halaka mutane 14, galibinsu 'yan darikar da Sheikh Dahiru Bauchi ke jagoranta.
A daya bangaren kuma, shi ma tsohon shugaban kasar Najeriya, kana jigo a jam'iyyar hamayya ta APC Manjo janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya tsallake rijiya da baya a hari na biyu da aka kai a kusa da gadar Kawo da ke dab da wani sansanin soja.
Rahotanni na cewa, an kai galibin gawawwakin wadanda hare-haren suka rutsa da su zuwa asibitin sojojin Najeriya da ke Kaduna da kuma sauran asibitoci da ke jihar.
Yanzu gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garin na Kaduna don hana barkewar wani tashin hankali, kana ta bayyana hare-haren a matsayin na matsorata, tare da bayyana kudurin cewa, gwamnatin za ta kamo wadanda suka kaddamar da hare-haren. (Ibrahim)