An bayyana kyautata ingancin hajojin nahiyar Afirka, musamman wadanda suka shafi noma, da kere-kere, da harkar ba da hidima a matsayin babbar hanyar bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Babbar darakta a cibiyar cinikayya ta duniya Arancha Gonzalez ce ta bayyana hakan a jiya Talata, yayin bikin bude taron kasa da kasa game da bunkasa hada-hadar fidda kayayyaki da ke gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda.
Daraktar cibiyar ta ITC ta ce, ko da yake a baya fannonin hakar ma'adanai na kan gaba a samarwa Afirka kudaden shiga, a yanzu nahiyar na da manyan hanyoyin bunkasa tattalin arziki da suka hada da harkokin kula da lafiya, da yawon shakatawa, da fasahar sadarwa da kuma ilimi, fannonin da a cewarta za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa manya, da ma kananan kasashe kamar Rwanda.
Gonzalez ta kara da cewa, kasancewar tuni Afirka ta zamo babbar kasuwar da duniya ke mai da hankali gare ta, lokaci ya yi da za a zage damtse wajen samar da karin ayyukan yi, da ci gaba daga dukkanin hanyoyi karkashin wannan dama.
Shi kuwa a nasa tsokaci, shugaba Paul Kagame na Rwanda, kira ya yi ga kasashen Afirka da su kara kwazo wajen gina rayuwar bil'adama, ta hanyar samar da karin guraben ayyukan yi, ta yadda za a kai ga samar da kyakkyawan yanayin bunkasar tattalin arziki, wanda zai yi gogayya da takwarorinsa na ragowar sassan duniya. (Saminu)