Shugaba Obama na Amurka ya ce, cutar Ebola dake ci gaba da hallaka rayukan al'umma a wasu kasashen yammacin Afirka na neman shallake hankali, duba da yadda yaduwar ta ke barazana ga tsaron duniya baki daya.
Obama wanda ya yi wannan tsokaci yayin ziyarar da ya kai cibiyar bincike da hana yaduwar cututtuka dake jihar Atlanta, ya kara da cewa, idan ba a kai ga dakile yaduwar cutar a yanzu ba, mai yiyuwa ne a samu karin dubban al'umma da za su harbu a nan gaba, matakin da a cewar sa ka iya haddasa mummunan sakamako ga tattalin arziki, da tsaro, da ma yanayin siyasar duniya.
Wannan ziyara ta shugaban na Amurka ta zo ne a gabar da ya ba da umarnin tura wasu dakaru 3,000 yammacin Afirka, domin taimakawa yakin da ake yi da cutar ta Ebola.
Kakakin fadar White House Josh Earnest, ya ce, dakarun za su ba da tallafi a fannin tsare-tsare da aikin injiniya, dake da alaka da ayyukan kiwon lafiya, maimakon kula da marasa lafiya kai tsaye. (Saminu)