Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da batan wani jirgin saman yakin ta kirar "Alpha Jet" mai dauke da matukansa su biyu, bayan tashinsa daga wani sansani dake birnin Yolan jihar Adamawa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun dakarun rundunar Mr. Chris Olukolade ya fitar, ta ce, jirgin na gudanar da ayyukansa na sintiri ne da safiyar ranar Juma'a kafin daga bisani a neme shi a rasa.
Sanarwar ta ce, duk wani yunkuri na gano inda jirgin ya shige ya ci tura, sai dai ana sa ran fara laluben inda jirgin ya shiga ba da wani bata lokaci ba. Amma ba a bayyana ko ana amfani da wannan jirgi ne, wajen yaki da kungiyar nan ta Boko Haram ba.
A 'yan watanni ukun da suka gabata dai mayakan kungiyar ta Boko Haram mai sansani a sassan arewa maso gabashin Najeriyar ta mamaye wasu kauyuka da garuruwa a jihar Borno mai iyaka da kasar Kamaru, inda ta ayyana kafa daular musulunci a wuraren.
Har wa yau kungiyar ta dauki alhakin kaddamar da hare-hare da dama a yankin na arewa maso gabashin kasar, musamman ma a garuruwan dake kudancin jihar Borno. Hakan kuwa na zuwa ne a gabar da dakarun sojin kasar ke matsa kaimi wajen kai farmaki maboyar 'ya'yan kungiyar, da sansanonin su ta kasa da sama. (Saminu)