Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya bayyana a ranar Litinin cewa, yana damuwa sosai da halin da ake ciki bisa karuwar yawan tashe-tashen hankali da yawan fararen hula dake mutuwa ko jikkata a kasar Libya, musammun ma a Tripoli, babban birnin kasar.
A cikin wata sanarwa ta kakakinsa, mista Ban ya yi kira ga bangarorin da wannan rikici ya shafa da su kai zuciya nesa da kuma kauracewa duk wani tashin hankali domin cimma muradin siyasa da zaman lafiya.
A cewar kafofin watsa labaran kasar, an yi musayar wuta a ranar Lahadi da safe a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Tripoli, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9 da jikkata 25, kuma 'yan kwanakin baya bayan nan, an yi bata kashi tsakanin gungun kungiyoyin kishin islama masu makamai da mayakan sa kai na birinin Zintan dake kudu maso yammacin Libya.
Shugaban MDD ya nuna cewa, wadannan tashe-tashen hankali na kawo koma baya ga kokarin 'yan kasar Libya na lokacin juyin juya hali domin kafa wata kasa mai 'yanci da walwala. Mista Ban Ki-moon na jaddada muhimmancin kafa tsarin shawarwari tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a Libya domin cimma wata mafita cikin lumana da za ta taimakawa mulkin wucin gadi na siyasa a wannan kasa, in ji kakakin Ban Ki-moon. (Maman Ada)