in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya kara wa'adin takunkumin da ya kakabawa Liberia
2013-12-11 10:41:22 cri

A ranar Talata ne kwamitin sulhu na MDD ya kara wani wa'adin shekara guda kan takunkumin da aka kakabawa kasar Liberia dangane da yakin basasar kasar da kuma zargin da kwararru dake sa-ido suka yiwa kasar na rashin bin ka'idojin da aka cimma.

Kwamitin ya ce, duk da ci gaban da aka samu a kasar, har yanzu ana zaman dar-dar a kasar, lamarin da ke ci gaba da haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya da ma shiyyar baki daya.

Don haka, tun daga ranar Talata, kwamitin ya yanke shawarar kara sabunta wa'adin takunkumi kan kasar ta Liberia, wadanda suka hada da haramtawa wasu dai-daikun mutane yin tafiye-tafiye tare da bin umarnin shawarar da tawagar kwararru suka bayar.

Kwamitin sulhun ya bukaci dukkan kasashe da kuma gwamnatin Liberia, da su baiwa tawagar da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya nada da farko a watan Yulin shekara 2007 cikakken hadin kai, wadda aka dora mata alhakin yin tattaki zuwa kasar Liberia da sauran kasashe makwabta, don yin nazarin yadda ake aiwatar da shirin tare da bayar da rahoto akai.

Bugu da kari, kwamitin ya bukaci gwamnatin kasar Liberia, da ta bullo da dokokin da suka dace a nata bangaren don kawo karshen fataucin makamai a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China