A yau Laraba 27 ga watan nan da safe, a yayin taro karo na 31 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 11, an tabbatar da iznin wakilcin mutane 2987 cikin wakilan majalisar wakilan jama'ar Sin karo na 12. Daga baya, zaunannen kwamitin ya gabatar da takardar dake kunshe da jerin sunayensu.
Wannan ya kasance karo na farko da aka zabi wakilai bisa adadin mutane a birane da kyauyuka, tun bayan da aka kyautata dokar zabe a shekarar 2010. Sakamakon ya nuna cewa, an zabi wakilai daga dukkan yankuna, kabilu da na fannoni daban-daban yadda ya kamata, musamman ma adadin ma'aikata, da manoma ya karu sosai, inda yawan mata da suka zama wakilai ya karu, aka kuma rage yawan wakilai daga jami'an jam'iyya da na gwamnati, tsarin wakilai ya kara samun kyautatuwa. (Amina)