in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na shirin gudanar da sauye sauye ga majalissar zartaswa
2013-03-10 16:36:06 cri

Majalissar zartaswar kasar Sin na shirin fara yin kwaskwarima ga sassan hukumomin gwamnati a karo na 7 cikin shekaru 30. Wannan dai mataki ya biyo bayan tsarin gyaran fuska ne da aka gabatar gaban zauren majalissar kasar ranar Lahadin nan 10 ga watan Maris.

Bisa kunshin sauye-sauyen dai ana sa ran rage tsoma hannun sassan hukuma cikin huldodin kasuwanci da harkokin da suka shafi zamantakewar al'umma. Haka nan za a rage yawan ma'aikatun gwamnatai dake karkashin kulawar majalissar zartaswar kasar daga 27 zuwa 25, yayin da kuma ake fatan yin kwaskwarima ga wasu hukumomi, da cibiyoyin ayyukan gwamnatin.

Daukar wannan mataki dai na da muhimmanci ga ayyukan sauye sauye, da na karfafa tasirin majalissar zartaswar kasar.

Baya ga wadancan sassa, ita ma ma'aikatar lura da sufurin jiragen kasa, dake kuma ke aikin sanya ido a sashen, a yanzu zata koma karkashin ikon sashen lura da harkokin mulki da na cinikayya.

Haka zalika ma'aikatar kula da kiwon lafiyar, da ta lura da yawan al'umma, da kuma ta kula da ayyukan kayyade iyali, za a hada su cikin sabuwar hukumar lafiya da kayyade iyali. Sai kuma ma'aikatar lura da ingancin abinci da magunguna, wadda za a daga martabar ta, zuwa babbar hukuma domin dada samar da damar kyautata nagartar abinci da magungunan, da al'ummar kasar ta Sin ke amfani dasu.

Ita ma hukumar lura da tekun kasar za ta samu karin karfin gudanar da nata ayyuka, bayan hade sassan rundunonin dake da alaka da ita karkashin inuwar hukuma guda da ake burin aiwatarwa.

Ban da wannan kuma akwai hukumar makamashin kasar, wadda za ta dauki nauyin aiwatar da manufofin mulki, da bada jagoranci a sashen na makamashi. Yayin da babbar hukumar lura da harkokin yada labaru da dab'i, da kuma hukumar kura da gidajen radio, da finafinai da gidajen talabijin, zata hade zuwa hukuma guda, wadda zata rika sanya ido kan dukkanin harkokin yada labarai, da dab'i, da dukkanin harkokin da suka shafi gidajen talabijin da Radio, da kuma fina finai.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China