in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da hari kan tawagar ma'aikatan jin kai a CAR
2014-04-30 09:58:47 cri

Ofishin MDD ya bayyana matukar takaici, game da harin gurneti da aka kaiwa tawagar ma'aikatan jin kai, dake yunkurin sauyawa musulmi 'yan gudun hijira guri a arewacin kasar Afirka ta Tsakiya CAR.

Harin dai wanda ake kyautata zaton mayakan sa kai na kiristoci da aka fi sani da Anti-balaka ne suka kaddamar da shi, ya haddasa mutuwar mutane biyu, tare da jikkata wasu karin mutane 6.

Wani mai magana da yawun MDD ya shaidawa manema labaru cewa, tawagar jami'an jin kan na kunshe ne da musulmi 1,300 da rikicin kasar ya ritsa da su lokacin da 'yan Anti-balakan suka jefa musu gurneti.

Su dai magoya bayan wannan kungiya ta kiristoci na dauki ba dadi ne da kungiyar musulmi 'yan tawaye ta Seleka, wadda ta jagoranci kifar da gwamnatin kasar a shekakar 2012. Rikicin da kuma tun daga waccan lokaci kawo yau, ya sabbaba raba dubban mutane da gidajensu, baya ga wasu sama da miliyan 2.2 da yanzu haka ke matukar bukatar agajin jin kai. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China