A halin da ake ciki, mutane kimanin dubu 250 suka tsere daga gidajensu a sakamakon mummunan artabun da ake yi a manyan garuruwan kasar Libya a baya bayan nan.
Wani rahoton hadin gwiwa wanda ya fito daga dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake Libya UNSMIL, da kuma ofishin kare hakkin bil'adama na kasar ta Libya, ya ce, a kalla mutane dubu dari sun rasa muhallansu a cikin kasarsu, kana kuma kimanin wasu mutanen dubu 150, wadanda suka hada har da kwararru daga kasashen ketare, sun fice daga kasar a yayin da kungiyoyin da ke fada da juna, ke ci gaba da arangama domin kokowar kama madafun iko a biranen Tripoli da Benghazi.
Rahoton ya ce, mayakan Islama, da wadanda ke kokarin kafa gwamnati wacce ba ta da nasaba da addini, sun kaucewa yin la'akari da rayukan fararen hula, a yayin da suke ta fada, ba ji ba gani, kuma da yawa daga cikin su ba su da isasshen horo, da sanin ya kamata, kuma yin amfani da makaman da suka sami illa ya haifar da samun kuskure wajen harbi da irin wadannan makaman, hakan ya jefa rayuwar farar hula, cikin hadarin gaske.
Kasar Libya dai ta samu karuwar tashe-tashen hankula tun bayan tashin hankalin shekarar 2011, wanda ya haddasa tunbuke gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi. (Suwaiba)