in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban UNGA ya yi kira da a tsai da kuduri ga jadawalin aikin ci gaba bayan 2015
2014-09-12 10:20:45 cri

Babban jami'i a ofishin jadawalin kasa da kasa na MDD a ranar Alhamis din nan 11 ga wata ya yi kira ga dukkan kasashe mambobin majalissar da su tsara wani shiri da zai mai da hankali da kuma samar da ayyukan da za'a yi na ci gaban duniya baki daya bayan shekara ta 2015, domin a samu ci gaba, a kuma kammala abin da aka fara a shirin muradun karni MDGs.

Shugaban ofishin na UNGA John Ashe ya yi kira a babban taron majalissar dake dauke da mambobi 193 a lokacin jawabinsa na kawo karshen wa'adin shugabancin wannan ofishi na tsawon shekara daya, inda aka yi nazarin jadawalin ayyukan da za a iya aiwatarwa na ci gaban kasashe bayan shekara ta 2015.

Mr. John ya ce, babban zaman taron na wannan karon a kan ayyukan bayan 2015 da mambobi za su yi nazari a kai zai wakilci ra'ayin mahalarta taron gaba daya wanda ya kamata ya kawo karshen talauci, ya kuma tabbatar da cewa, an samu shirin ci gaba mai dorewa, sannan kuma wannan shiri ya karbu a dukkan kasashen duniya. Yana mai bayanin cewa, shirin ya kamata ya ci gaba daga inda shirin muradin karni ya tsaya, ya kuma cike gurbin da ya bari, sannan ya dauka zuwa wani sabon matsayi.

Mr John ya jaddada cewa, shirin na bayan shekarar 2015 zai zama shiri ne da ya wuce ra'ayoyin ya kai ga cewa, yana da matsaya da kuma hangen nesa wajen ayyukan da suka kamata.

Ya lura da cewa, ofishin UNGA ya amince da shawarwarin da kwamiti na musamman game da tsara sabon shirin ya gabatar mai take ci gaba mai dorewa wato SDGs wanda zai fitar da jerin ayyukan da za su tabbatar da wannan kuduri. Shirin SDGs da za'a dasa a kan MDGs zai kunshi bangarorin tattalin arziki da muhalli. Wadanda za su duba ci gaba a bangaren makamashi, tattalin arziki, rashin daidaito, birane, dorewar samun ci gaba da samar da ababen bukata, da kuma zaman lafiya a cikin al'ummomi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China