in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya da su kara kwazo domin cimma nasarar shirin MDGs
2013-12-21 16:46:38 cri
Babban magatakarda na MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga daukacin kasashen duniya, da su zage damtse wajen tabbatar da nasarar shirin cimma muradun MDGs a takaice, tare da batun tsara shirin neman samun bunkasuwa na duniya bayan shekarar 2015.

Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na bikin ranar hadin gwiwar al'ummar duniya dake wakana a ranar 20 ga watan Disamba na ko wace shekara. A jawabin nasa Mr. Ban ya ce, shugabannin kasa da kasa sun tabbatar da cewa, kokarin cimma nasarar shirin na MDGs, ba zai kai ga nasara ba, sai da girmama juna, da daukar nauyi tare.

"A yau ranar hadin gwiwar bil'Adam ta duniya, mun yanke shawarar hada karfi da karfe tare, domin rage gibin dake tsakanin al'ummu a fannin cimma wannan nasara, tare da tsara hanyar da za a bi bayan shekarar 2015, da fatan samar da makoma mai dorewa ga kowa da kowa." in ji Ban Ki-moon.

Ban da wannan, Ban Ki-moon ya kara da cewa, game da batun tinkarar kalubale a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da muhalli, da kuma zamantakewar al'umma, kamata ya yi kasashen duniya su bayar da gudummawarsu, da samar da kudaden da za a kashe a fannin bunkasa kasashe gwargwadon karfinsu, domin cimma gajiyar sakamako mai kyau. Babban magatakardar MDDr ya kuma jaddada cewa, wannan ne ainihin adalci da daidaito da ake fata samu, kuma shi ne ma'anar hadin gwiwa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China