in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiwatar da matakan yaki da ta'addanci a Sin
2014-05-26 10:16:40 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Sin ta fara aiwatar da matakan yaki da ta'addanci na tsahon shekara guda, aikin da ake fatan zai mai da hankali ga dakile yaduwar kungiyoyin tada-kayar-baya, da hana kera muggan makamai wadanda masu tsattsauran ra'ayi ke amfani da su, da kuma rushe wuraren horas da 'yan ta'adda.

Ma'aikatar tsaron al'ummar kasar ta Sin ce ta bayyana fara daukar wannan mataki tun daga Juma'ar da ta gabata. Tuni kuma ma'aikatar ta umarci jami'anta dake yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kansa, da su yi hadin gwiwa da jami'an tsaro dake sauran sassan kasar domin cimma nasarar wannan aiki.

A wani ci gaba kuma, rundunar 'yan sanda dake yankin na Xinjiang Uygur, ta ce, ta samu nasarar gano wasu kungiyoyin kaifin kishin addini 23, yayin wani simame da jami'anta suka gudanar a yankin na arewa maso yammacin kasar Sin.

A cewar ofishin lura da harkokin tsaron al'ummar yankin, an cafke sama da mutane 200 a yankunan Hotan, da Kashgar da kuma Aksu, yankunan dake da yawan mabiya addinin musulunci. Kaza lika 'yan sandan sun ce, sun amshe ababen fashewa sama da 200, yayin da suke gudanar da aiki a yankin.

Tuni dai ofishin kula da harkokin shari'ar yankin, da hadin gwiwar ofishin lura da harkokin tsaron al'ummar yankin suka fidda wata sanarwa, wadda ke kira ga masu data-zaune-tsaye da su mika kansu ga hukuma, domin fuskantar hukunci mai sauki. Sanarwar ta kuma ja kunnen al'ummar yankin da su kauracewa shiga kungiyoyin ta'adda, ko marawa masu baya.

Bugu da kari, sanarwar ta jaddada batun haramta tallafawa irin wadannan kungiyoyi ta kowace irin hanya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China