Jagororin rundunonin 'yan sanda na kasashen dake nahiyar Afirka, sun amince da kafa dunkulalliyar hukumar 'yan sanda ta hadin gwiwar nahiyar mai lakabin Afripol, yayin taron da ya gudana a Algiers, babban birnin kasar Aljeriya.
Da yake karin haske ga manema labaru don gane da hakan, shugaban rundunar 'yan sandan kasar Aljeriya Manjo Janar Abdelghani Hamel, ya ce, wannan kuduri na da nufin kafa wani tsari da zai ba da dama ga rundunonin 'yan sandan dake nahiyar su yi aiki tare, gami da musayar muhimman bayanai da dabarun inganta tsaro.
Yayin taron wanda kasar Aljeriya ta dauki nauyin shiryawa, wakilansa, a ta bakin Janar Hamel sun yi amannar cewa, sabon shirin kafa hukumar 'yan sandan Afirkan zai karfafa ayyukan 'yan sanda a fannonin samar da horo, da inganta dabarun bincike na kimiyya, bisa doron doka da mutunta hakkokin bil'adama.
Bugu da kari, Janar Halem ya ce, kasarsa za ta bukaci kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ta sanya wannan kuduri, cikin ajandar babban taronta dake tafe cikin watan Yunin wannan shekara da muke ciki. (Saminu)