in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu gungun kungiyar Islama sun mamaye ofishin jakadancin Amurka a Libya
2014-09-01 11:54:11 cri

Wasu gungun mayakan Islama sun kai farmaki, tare da mamaye ofishin huldar jakadancin kasar Amurka dake Tripoli, babban birnin kasar Libya, inda a yanzu haka ake ci gaba da tabka kazamin fada a farfajiyar babban birnin na Tripoli.

Wata majiya ta jami'an tsaro, wacce ta ba da labarin abin da ya wakana, ta ce, a yayin da 'yan tsageran suka kutsa kansu cikin ofishin jakadancin Amurka sun mamaye babban ginin dake cikin harabar ofishin jakadancin.

Daya daga cikin kwamandojin mayakan Islaman ya tabbatar da aukuwar hakan, to amma jakadar ofishin jakadancin Amurka dake Libya Deborah K. Jones, ta ce, ta ga hoton abin da ke faruwa a Libya, amma ta ce, hoton bidiyon ya nuna cewar, an dauki hoto ne a wani karamin ofishin huldar jakadancin na Amurka dake can Libya, amma ba za ta iya tantance hakan ba, tun da a yanzu tana kasar Malta da zama.

Tun dai a watan Yuli ne, ofishin jakadancin na Amurka dake Libya, ya kwashe dukkanin ma'aikatansa, a yayin da fada ya yi kamari tsakanin kungiyar Islama masu dauke da makamai da kuma kungiyoyi wadanda ke muradin kafa gwamnati, wadda ba ta da nasaba da addini. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China