Mukaddashin babban jami'in rundunar 'yan sandan Najeriya Emmanuel Ojukwu, ya ce, ana ci gaba da tsananta binciken gano jami'an rundunar su 35 da suka bace, biyowa bayan farmakin baya bayan nan da 'yan Boko Haram suka kaddamar a barikin su dake garin Gwoza.
Wata majiyar rundunar 'yan sandan ta ce, 'yan sandan sun bace ne, tun ranar 20 ga watan nan na Agusta, sakamakon farmakin da 'yan Boko Haram suka kaddamar a barikin horas da su dake garin na Gwoza a jihar Borno. Kafin hakan dai sai da kungiyar ta kaddamar da wani harin na daban a wannan bariki a ranar 7 ga watan na Agusta.
Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriyar ta fitar da wata sanarwa, dake bayyana aniyarta ta tabbatar da kubutar da jami'an nata. Inda sanarwar ta kara da cewa, akwai fatan samun nasarar wannan buri da aka sanya gaba.
Kaza lika sanarwar ta ce, wani bincike da ta gudanar ya ba ta damar gano wasu daga jami'an nata. (Saminu)