Kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da sassan da ba sa ga maciji da juna a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR suka sanya wa hannu, matakin da kwamitin ke fatan zai kai ga sasantawa da sake gina kasar.
Wata sanarwa da mambobin kwamitin suka bayar ta jaddada bukatar magance hakikanan abubuwan da ke haddasa tashin hankali a kasar ta hanyar sasantawa a siyasance, yakar duk wani kokari na nuna bambance-bambance, kwance damarar makamai, sake gina hukumomin gwamnati da aka lalata.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta tsunduma cikin rikicin kabilanci ne tsakanin 'yan tawayen Seleka da na anti-Balaka, bayan da aka hambarar da gwamnatin kasar a watan Janairun shekarar 2014, inda aka yi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan 2.2 ne ke bukatar agajin jin kai, sakamakon rikicin da ya barke a kasar.
A ranar Laraba ne wakilan tsoffin kungiyoyin 'yan tawayen Seleka da na anti-Balaka da kuma na gwamnatin wucin gadin kasar suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaida bude wuta a Brazzaville, babban birnin kasar jamhuriyar Congo da nufin kawo karshen tashin hankalin da kasar ke fuskanta. (Ibrahim)