Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu za ta ci gaba da bin tsarin da zai sa ta iya tsimin kudi lokacin da ya kamata domin ta yi amfani da shi a wani lokacin da bukatar hakan zai kawo daidaito ga tattalin arzikinta, in ji mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa a jiya Alhamis.
Mr. Ramaphosa wanda yake bayyana hakan a babban taron da bankin tsimin na kasar ta shirya a Muldersdrift dake wajen birnin Johannesburg, ya ce, hakan na daya daga cikin niyyar gwamnatin wajen yin kwaskwarima mai karfin gaske da zai kawo sauyi a tattalin arzikin kasar, kuma zai zama wani tsari da ya banbanta da ko wane iri.
Ya ce, gwamnati na neman tsarin da zai sauya daga kashe kudi, a mai da su a hanyar zuba jari.
Gwamnati, in ji mataimakin shugaban kasar, ta hango wata babbar daman, a inganta cibiyoyin tattalin arziki yadda za su taimaka wajen zuba jari a ababen more rayuwa, bangaren noma, kananan masana'antu, da tsarin ba da kafar ciyar da kai gaba a bangaren tattalin arziki, da ma masana'antu.
A wassu lokuta, wannan aiki ba ya bukatar wata sabuwar dabara, sai dai a inganta wadanda ake da su a kasa, in ji Mr. Ramaphosa. (Fatimah)