Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Lesotho, yana mai kira ga daukacin sassan da batun ya shafa, da su rungumi matakan warware banbancin dake tsakanin su ta hanyar lumana.
Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya kuma bayyana bukatar mutunta kundin tsarin mulkin kasar, tare da kiyaye doka da oda.
Daga nan sai ya jinjinawa kungiyar bunkasa kasashen kudancin Afirka ta SADC, da kungiyar Commonwealth, da sauran kungiyoyin dake tallafawa kasar ta Lesotho a kokarinta na warware sa-in-sar dake wanzuwa tsakanin wakilan gwamnatin hadakar kasar.
A ranar Asabar din, karshen makon jiya ne dai firaministan kasar ta Lethoso Tom Thabane, ya tabbatar da aukuwar jiyun mulkin da sojojin kasar suka yi, bayan da ya tsallake zuwa kasar Afirka ta Kudu.
Kasar Lesotho dai ta sha fama da juyin mulkin sojoji a lokuta da dama, tun bayan samun 'yancin kanta a shekarar 1966. (Saminu)