Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira da babbar murya ga Isra'ila da Palastinu, da su amince da shawarar tsawaita wa'adin dakatar da kai wa juna hare-hare.
Mr. Ban wanda ya bukaci a tsawaita wa'adin da sa'o'i 24, ya ce, hakan zai ba da damar shigar da karin kayayyakin agajin jin kai.
Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar ta nanata muhimmacin dake akwai, na tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, duba da a cewar sanarwar, dauki ba dadin da ya gabata ya janyo asarar rayukan mutane da yawa, tare da jefa da dama cikin mawuyacin hali.
Har wa yau sanarwar ta bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki a Gabas ta Tsakiya, da ma na sauran kasashen duniya, da su ba da tallafi wajen ganin an shigar da muhimman kayayyakin jin kai wuraren da ake bukatar su.
Rahotanni dai sun ce, an hallaka wani Bafalasdine daya, aka kuma jikkata wasu Falasdinawan 10, lokacin da wani jirgin saman yaki na Isra'ila ya kai farmaki a ranar Lahadi, lamarin da ya kawo karshen kudurin tsagaita wuta na sa'o'i 42 da MDD ta gabatar ga sassan biyu. (Saminu)