Wani rukunin sojojin ruwan kasar Sin ya ajiye kayansa a Victoria Bay, dake birnin Cape Town a wani rangadin karshe da ya kai shi zuwa kasashen Afrika takwas, tare da samun tarbo da wajen mutane fiye da dubu daya.
Babban ofisa, Amiral Robert Higgs na sojan ruwan Afrika ta Kudu ya bayyana a cikin jawabinsa na tarbon bakin cewa, wannan ziyara na bayyana abokantaka da dangantaka tsakanin sojojin ruwan kasashen biyu.
Ofisan ya bayyana cewa, a yayin wannan ziyara, za'a gudanar da ayyukan daban daban tsakanin Escort Task Group da sojojin ruwan kasar Afrika ta Kudu.
Haka kuma 'yan Afrika ta Kudu za su iyar kai ziyarar gani da ido a cikin jiragen ruwan kakkabo koka biyu na zamani.
Kasashen biyu za su iyar taimakawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya a wannan shiyya, da ma duniya baki daya, in ji Amiral Higgs.
A nasa bangare, jakadan kasar Sin dake Afrika ta Kudu, mista Tian Xuejun ya bayyana cewa, wannan ziyara ta zo daidai a lokacin da kasar Sin da Afrika suke samun babban cigaba cikin sauri da karfi ta bangaren huldar dangantaka bisa manyan tsare-tsare, musamman ma tsakanin Sin da Afrika ta Kudu da aka kafa tun yau da 'yan shekaru. (Maman Ada)