in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar dala miliyan 600 wajen yaki da Ebola, in ji WHO
2014-09-04 10:16:51 cri

Babbar darakta a hukumar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan, ta ce, yanzu haka ana bukatar samar da kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 600 domin inganta aikace-aikacen yaki da cutar Ebola.

Chan wadda ta bayyana wa wani taron manema labarai hakan a birnin Washington na kasar Amurka, ta ce, cutar Ebola na yaduwa tamkar wutar daji a wasu kasashen dake yammacin Afirka, don haka ya zama wajibi a zage damtse wajen dakile ta.

Kaza lika babbar daraktar ta WHO ta ce, bullar cutar a wannan karo ita ce mafi muni da aka taba gani a tarihi cikin kusan shekaru 40 da gano ta. Chan ta ce, ya zuwa makon nan da muke ciki, akwai mutane dake dauke da cutar, ko ake zaton sun kamu da ita kusan 3,500, yayin da kuma tuni sama da mutane 1,900 suka rasu sakamakon harbuwa da cutar.

Da take tsokaci game da tallafin da aka samu a fagen yaki da cutar kuwa, Chan ta jinjinawa tallafin da kasashe irin su Amurka da Birtaniya, da Sin, da Canada, Afirka ta Kudu, da Switzerland, da Faransa, da kuma Kuwait suka bayar. Har wa yau ta gode wa gwamnatin kasar Sin, sakamakon tallafin kwararru da na kayayyakin aiki da ta samar ga kasashen da suka fi fama da cutar ta Ebola. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China