in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta dakatar da tura jirgin ruwan yaki zuwa Rasha
2014-09-04 10:44:59 cri

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce, kasarsa ta dakatar da tura daya daga cikin jiragen yakin da za ta tura zuwa kasar Rasha, duk da yiwuwar samun tsagaita bude wutan a gabashin Ukraine.

Shugaban ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, yana mai cewa, matakin Rasha a Ukraine tamkar juya baya ne ga kiraye-kirayen da kasashen Amurka da Buraniya suka yiwa Rasha game da abin da faruwa a gabashin Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha Itar-Tass, ya ruwaito ministan tsaron kasar Rasha Yuri Borisov na cewa, Rasha na ganin shawarar kasar ta Faransa na dakatar da tura jirgin ruwan yakin zuwa Moscow, ba zai yi mata wata illa ba. Ko da yake hakan na iya raunata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China