in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta rufe ofishin jakadancinta a Libya
2014-07-31 09:55:53 cri

Faransa ta rufe ofishin jakadancinta a Libya, tare da kwashe ma'aikatanta sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a kasar dake arewacin Afrika.

Kamar yadda wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce, an rufe ofishin jakadancin dake Tripoli ne na wucin gadi, ganin yadda sha'anin tsaro ya tabarbare, amma duk wata huldar jakadanci da kasar ta Libya, za ta aiwatar da ita daga birnin Paris.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, an dauki dukkan matakan da ya kamata na ganin cewa, sauran jama'arta da har yanzu suke zaune a Libya su koma gida lafiya cikin wani dan lokaci, duk da cewa, ba'a ba da adadin 'yan kasar da suka saura a Libyan mai arzikin mai ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China