in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa za ta tura karin dakaru zuwa arewacin Afrika don magance barazanar 'yan ta'adda
2014-07-14 09:49:23 cri

Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a jiya Lahadi ya sanar da cewa, kasarsa za ta tura karin sabbin dakaru 3,000 zuwa yankin Sahel inda za su dakile masu tsattsauran ra'ayi.

Da hadin gwiwwar kasashe biyar a wannan yankin, ayyukan dakile ta'addancin zai fara a kwanakin nan masu zuwa, inda za su yi aiki da jiragen sama marasa matuka, jiragen sama masu saukar ungulu da kuma jiragen yaki domin tabbatar da nasarar abin, in ji Le Drian.

A wata ganawa da kafar yada labarai na kasar Erope1, ministan ya ce, ayyukan sojojin kasar a arewacin Mali na da nufin taimakawa mahukuntar wannan kasa ce su kawo karshen ayyukan masu tsattsauran ra'ayi, daga baya sai dakarun yaki da ta'addanci mai lakabin Barkhane, wanda musamman aka kafa shi don wannan shiyya su ci gaba da gudanar da sauran ayyukansu na yaki da ta'addanci a yankin Sahel. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China