in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta bukaci 'yan kasar da su fice daga Libya sakamakon rikici
2014-07-28 09:56:10 cri

Kasar Faransa a ranar Lahadin nan 27 ga wata ta bukaci mutanen kasar dake zaune a kasar Libya da su fice daga kasar sakamakon mummunar tashin hankali da ake fuskanta, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar tana mai bayanin cewa, ta riga ta tuntubi dukkanin 'yan kasarta da su yi hanzarin tuntubar ofishin jakadancinta dake birnin Tripoli.

A cikin makonni biyu da suka gabata, Libya ta tsunduma cikin mummunar tashin hankali tsakanin masu tsattsauran ra'ayin addini da sojojin gwamnati a babban birnin na Tripoli, da kuma birni mafi girma na biyu Benghazi, inda sama da mutane 150 suka rasa rayukansu.

Bayan tsanantar rikicin, Amurka, MDD da Turkiya su ma sun janye ma'aikatan diplomasiyarsu daga Libya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China