in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi tir da hari kan tawagar ma'aikatan MINUSMA
2014-09-03 09:49:10 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi matukar Allah wadai da kisan wasu jami'an tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA su 4 a kasar Mali, sakamakon tashin wata nakiya da aka dana kan titi, wadda ta tashi da motar da suke ciki a yankin Kidal dake arewacin kasar.

Rahotanni dai sun ce, ma'aikatan su 4 'yan asalin kasar Chadi sun rasa rayukansu ne nan take, sakamakon fashewar da ta tarwatsa motar dake dauke da su, baya ga wasu 15 da suka ji munanan raunuka. Da ma dai wannan yanki na Kidal yanki ne da 'yan tawayen kasar ke da karfi matuka, tun bayan yunkurin juyin mulkin kasar na shekarar 2012.

Cikin wata sanarwa da babban magatakardar MDDr ya fitar game da wannan batu, ya bayyana alhininsa game da rasuwar ma'aikatan, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Mr. Ban ya ce, irin wadannan hare-hare ba za su sanyaya gwiwar MDD ba, a yunkurinta na ci gaba da tallafawa al'ummar Mali wajen dawo da managarcin yanayin zaman lafiya da lumana a dukkanin fadin kasar.

Wannan dai hari shi ne irinsa na baya bayan nan da ma'aikatan MINUSMAn suka fuskanta daga dakaru masu dauke da makamai cikin wannan mako. A 'yan kwanakin baya ma wasu maharan sun kai harin rokoki kan sansanin tawagar, baya ga wani harin bam na ranar 29 ga watan jiya, wanda ya jikkata jami'an MINUSMAn 'yan kasar Chadi su 9. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China