A kalla mutane takwas ne aka kashe a ranar Litinin da yamma a cikin wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wasu majiyoyi masu tushe a ranar Talata a birnin Abuja.
Haka kuma, mayakan sun lalata wata gadar dake hada yankunan dake nisa da Katarko a Gujba da sauran yankunan na jihar, in ji Liasu Auwal, wani mazaunin wurin da ya bukaci a sakaya sunansa.
Wata majiyar jami'an tsaro, ta bayyana cewa, aka fara kai hari ga wata makarantar horar da soja, kafin mayakan suka kawo rudani da fargaba a cikin al'ummar wurin, da kuma lalata gadar. Mutane da dama suka jikkata, in ji wannan majiya.
Yankin Katarko, na da nisan kilomita 25 daga birnin Damaturu, hedkwatar jihar Yobe, kuma ya kasance wata cibiyar mayakan kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)