Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD (HRC) ta amince da wani kuduri da ke allahwadai da yadda mayakan kungiyar IS da ke rajin kafa daular musulunci a kasar Iraki, da sauran kungiyoyi dangin wadannan ke take hakkokin bil-adama da dokokin kasa da kasa game da harkokin jin kai.
An amince da kudurin ne a wani zama na musamman da hukumar ta yi a ranar Litinin game da yanayin hakkokin bil-adama a kasar ta Iraki.
Bugu da kari kudurin ya yi allahwadai da yadda ake gallazawa jama'a saboda bambancin addini, ko kabila, da kuma yadda ake cin zarafin mata da kananan yara.
A halin da ake ciki, kudurin ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wa gwamnatin Iraki, ta yadda za ta kare tare da taimaka wa wadanda 'yan ta'adda suka tilasta musu barin gidajensu.
Bugu da kari kudurin ya bukaci ofishin kwamishinan kare hakkin bil-adama na MDD da ya hanzarta tura wata tawaga zuwa kasar Iraki da nufin binciko yadda mayakan na IS da sauran kungiyoyi mayaka suka keta hakkokin bil-adama da dokokin kare hakkin bil-adama na kasa da kasa don fito da wani rahoto game da binciken da suka gudanar da za a mika wa hukumar. (Ibrahim)